Rigakafin Cutar Daji

Rigakafin Cutar Daji
preventive medicine (en) Fassara
Bayanai
Object class of action (en) Fassara Sankara
Australian volunteer Laura Davidson worked to boost the profile of the Port Moresby Cancer Relief Society, 2011
Kid Chan National Cancer Society

Rigakafin Cutar Daji Ya kasan ce shi ne matakin farko da ake rage haɗarin cutar sankara da mace-macen da akeyi ta sanadiyyar ta.[1][2] rigakafin kuma ta dogara ne akan ƙoƙarin daidaita da kuma inganta salon rayuwa , da zamantakewar mutane da tattalin arziki ko manufofin jama'a masu alaƙa da rigakafin cutar kansa.[3] Ana ɗaukar rigakafin cutar kansa ta duniya a matsayin muhimmin maƙasudi saboda zartar da shi ga ɗimbin jama'a, da kuma rage tasirin kansa na dogon lokaci ta hanyar haɓaka ayyuka da ɗabi'un kiwon lafiya masu fa'ida, da fa'idar ingancin farashi da yuwuwan sa .[2]

Yawancin cututtukan daji na farawa ne daga tarin gurɓataccen muhalli wanda yana afkuwa ne ta hanyar lalacewar epigenetic , amma ba duka ba ne ake kamuwa da cutar kansan ta hanyar gurɓataccen muhalli.[4] Fiye da kashi 75 cikin 100 na mace-macen cutar daji za a iya kiyaye su ta hanyar guje wa abubuwan haɗari da suka haɗa da: taba, kiba, rashin isasshen abinci, rashin motsa jiki, barasa, da dai sauran su, cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i, da gurɓataccen iska.[5][6] Ba duk cututtukan kansar za a iya sarrafawa ba, irin abubuwan da ke faruwa ta zahiri da kuma sauran lokuta na ciwon daji ana haifar da su ta hanyar gado. Dabarun gyara kwayoyin halitta na yanzu da ke ƙarƙashin haɓakawa na iya zama matakan kariya a nan gaba.[7] Hakanan za'a iya inganta matakan rigakafin nan gaba kuma ta hanyar ingan tashi da haɓaka ƙayyadaddun abubuwa ta hanyar yin la'akari da tsarin halittar mutum ɗaya, wanda kuma aka sani da cutar kansa ta tushe."[2]

  1. "Cancer prevention: 7 steps to reduce your risk". Mayo Clinic. 27 September 2008. Retrieved 30 January 2010.Samfuri:Medrs
  2. 2.0 2.1 2.2 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Valle_20152
  3. "Cancer Prevention & Early Detection Facts & Figures 2017-18" (PDF). Cancer.org. April 1, 2017.
  4. Danaei G, Vander Hoorn S, Lopez AD, Murray CJ, Ezzati M (2005). "Causes of cancer in the world: comparative risk assessment of nine behavioural and environmental risk factors". Lancet. 366 (9499): 1784–93. doi:10.1016/S0140-6736(05)67725-2. PMID 16298215. S2CID 17354479.
  5. Doll R, Peto R (1981). "The causes of cancer: quantitative estimates of avoidable risks of cancer in the United States today". J. Natl. Cancer Inst. 66 (6): 1191–308. doi:10.1093/jnci/66.6.1192. PMID 7017215.
  6. Anand P, Kunnumakkara AB, Kunnumakara AB, Sundaram C, Harikumar KB, Tharakan ST, Lai OS, Sung B, Aggarwal BB (2008). "Cancer is a preventable disease that requires major lifestyle changes". Pharm. Res. 25 (9): 2097–116. doi:10.1007/s11095-008-9661-9. PMC 2515569. PMID 18626751.
  7. "CRISPR Gene-Editing Tool May Help Improve Cancer Immunotherapy". National Cancer Institute. 2017-03-20. Retrieved 2018-03-09.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search